logo

HAUSA

Sojojin Najeriya sun kashe a kalla ’yan ta’adda 50 a wasu samame

2023-10-13 10:27:37 CMG Hausa

A kalla 'yan ta'adda 50 ne aka kashe a hare-hare daban daban da dakarun gwamnati suka kai a yankin arewacin Najeriya a cikin makon da ya gabata, kamar yadda rundunar sojin ta bayyana a ranar Alhamis.

Kakakin rundunar, Edward Buba, ya shaidawa manema labarai a babban birnin tarayya Abuja cewa, sun kama ’yan ta’adda 114 a lokacin da suke gudanar da ayyukansu a yankin arewa a makon.

Buba ya ce, sojojin sun ceto a kalla mutane 49 da aka yi garkuwa da su a yankin arewa maso gabashin kasar, yayin da wasu shugabannin kungiyar ta Boko Haram suka mika wuya tare da ajiye makamansu saboda tsananin lugudan wuta daga sojoji.

Hare-hare daga ’yan ta’adda dai ya zama barazana ta farko ga tsaro a yankunan arewaci da tsakiyar Najeriya, lamarin da ya janyo asarar rayuka da kuma yin garkuwa da mutane a 'yan watannin nan. (Muhammed Yahaya)