logo

HAUSA

Tanadin kudin kasar Sin ya taka muhimmiyar rawa wajen samar da ‘yanci da ci gaban tattalin arziki mai dorewa da inganta rayuwar jama'a a Afirka

2023-10-13 21:54:18 CMG Hausa

A kwanan nan, kwalejin nazarin sabon tsarin tattalin arziki na jami’ar Peking ta kasar Sin ya fitar da wani rahoto mai taken “bincike kan ingancin tanadin kudade da Sin ta samar wa kasashen Afirka”. 

Game da rahoton, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin ya bayyana a yau Jumma’a cewa, rahoton ya dogara ne kan alkaluma da bayanai, dangane da yadda kasar Sin ke ba da tanadin kudi ga kasashen Afirka, ya kuma gano cewa, tanadin kudi da kasar Sin ke bayarwa, na taimakawa a fannonin ci gaban tattalin arzikin kasashen Afirka, inganta ababen more rayuwa, da kara samun kudin shiga na fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, da jawo jarin kasashen waje kai tsaye, da shigar da karin dalibai a makarantu, da samar da ayyukan yi da dai sauransu.

Sakamakon binciken ya sake nuna cewa, tanadin kudin da kasar Sin ke samarwa, ya taka muhimmiyar rawa wajen samun 'yancin kai da dorewar ci gaban tattalin arzikin Afirka da inganta rayuwar jama'a. Kasar Sin tana son ci gaba da yin hadin gwiwar samar da kudade bisa bukatun Afirka, tare da yin kira ga kasashen duniya da su kara taimakawa kasashen Afirka wajen samun ci gaba. (Safiyah Ma)