logo

HAUSA

Shugaban Najeriya ya nada sabon shugaban hukumar yaki da rashawa

2023-10-13 10:17:21 CMG Hausa

A jiya Alhamis ne shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu ya nada sabon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa a wani yunkuri na karfafa yaki da cin hanci da rashawa da tabbatar da gaskiya a Kasar da ta fi kowacce yawan al’umma a Afirka.

Nadin Ola Olukoyede a matsayin sabon shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC, ya fara aiki nan take, a cewar wata sanarwar da fadan shugaban kasar ta fitar.

Nadin Olukoyede ya biyo bayan murabus din tsohon shugaban hukumar ta EFCC, Abdulrasheed Bawa wanda ke tsare a hannun jami’an ’yan sanda farar kaya tun watan Yuni.

Tinubu, wanda ya hau kan karagar mulki a karshen watan Mayu, ya himmatu wajen farfado da kokarin Najeriya na yaki da cin hanci da rashawa da inganta gaskiya da rikon amana a tsakanin gwamnati da ma’aikatun gwamnati.

Shugaban na Najeriya har ila yau, ya nada Muhammad Hammajoda a matsayin magatakardan hukumar ta EFCC a ranar Alhamis din, yayin da ya bayyana hukumar a matsayin “wani muhimmin ginshiki” a gwamnatinsa”. (Yahaya)