logo

HAUSA

Sakatare Janar MDD ya yi bakin cikin matakin da Nijar ta dauka na korar mai gudanar da ayyukan hukumar a yankin

2023-10-12 10:17:57 CMG Hausa

A jiya Laraba ne kakakin Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya nuna bacin ransa kan matakin da gwamnatin mulkin sojan Nijar ta dauka na korar zaunannen jami’in gudanar da ayyukan MDD a Nijar.

Matakin dai ya kawo cikas ga ikon MDD na gudanar da muhimman ayyukan da kungiyar ta duniya ke yi ga al’ummar Nijar, inda miliyan 4.3 daga cikinsu musamman mata da kananan yara ke bukatar agajin jin kai, a cewar kakakin.

Dujarric ya ce, “Babban sakataren ya amince da tsarin MDD a Nijar.” Ya kuma jaddada cewa, umarnin korar jami’in daga kasar ya saba wa tsarin doka da ya shafi MDD, ciki har da wajibcin dake karkashin kundin tsarin MDD da kuma gata da kariya da aka baiwa kungiyar.

Kakakin ya kara da cewa, duk da wannan umarni, Guterres ya nanata kudurin MDD na ci gaba da kasancewa tare da kai dauki ga al’ummar Nijar, ta hanyar ci gaba da ayyukan jin kai da raya kasa. (Yahaya)