logo

HAUSA

Kamfanin Huawei ya kuduri aniyar habaka fasahar zamani ta dijital a Kenya tare da sabbin fasahohi

2023-10-12 11:19:04 CMG Hausa

A jiya Laraba ne Huawei, wani kamfanin sadarwa na kasar Sin ya kuduri aniyar taimakawa kasar Kenya wajen habaka hada fasahar zamani ta dijital, da tabbatar da fadada hanyoyin shiga yanar gizo da hanyoyin sadarwa ta hanyar samar da sabbin fasahohi.

Tony Li, babban jami'in fasaha na yankin kudancin Afirka na Huawei ne ya bayyana hakan a yayin wani taron shiyya-shiyya a Nairobi, babban birnin kasar Kenya. Ya yi nuni da cewa, kasar Kenya ta riga ta sami gagarumin ci gaba a cikin shekaru goma da suka gabata, tare da bullo da hanyoyin sadarwa na 4G da 5G, da kuma hanyoyin sadarwa na fiber don watsawa da kuma sadarwa ta karshe tsakanin mutane da na’ura.

"Muna nufin samar da sabbin hanyoyin samar da kayan aiki da manhajar sarrafa kwamfuta wadanda ke da sauki da sauri don sanyawa, kulawa, da sabuntawa," a cewar Li yayin taron koli na Conext Digital Infrastructure.

Taron da aka gudanar a cikin kwana daya, ya tattaro kwararru fiye da 100 kan fasahar sadarwa ta zamani da jami'an gwamnati daga gabashin Afirka, inda suka yi nazari kan ci gaban fasahar zamani a fannin tattalin arziki na zamani. (Muhammed Yahaya)