logo

HAUSA

NNPC: Nan da 2024 Najeriya za ta zama babbar dilla wajen fitar da man fetur zuwa ketare

2023-10-10 09:43:11 CMG Hausa

Kamfanin man fetur na Najeriya NNPC ya ce, yana da kwarin gwiwar cewa zuwa shekara ta 2024 Najeriya za ta kasance babbar dilla wajen hada-hadar cinikin tataccen man fetur zuwa kasashen duniya.

Babban shugaban hukumar gudanarwar kamfanin na NNPC Mele Kyari ne ya tabbatar da hakan yayin da yake jawabi wajen taron kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas na kasa a birnin Abuja, inda ya tabbatar da cewa, zuwa karshen wannan shekara ta 2023 matatun man kasar za su fara aiki gadan-gadan.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Mr Mele Kyari ya ce, samun karuwar rijiyoyin mai na doron kasa ya haska cewa Najeriya ta kama hanyar bunkasuwa a fagen harkokin masana’antun man fetur da iskar gas, inda ya ce matatun man kasar na fara aiki, Najeriya za ta fara sayar da tataccen mai ga wasu kasashen.

A kan yanayin da kasuwar man fetur a cikin gida yanzu ke ciki kuwa, shugaban kamfanin na NNPC ya ce, zai yi wahalar gaske a iya kayyade adadin man fetur da ake amfani da shi kullum a Najeriya, kasancewar yawan man fetur din da ake daukowa daga depo-depo na kasar ya ragu da kaso 30 tun bayan sanar da janye tallafin mai.

“Na sha fada a kullum cewa ba mu da bayanai na hakika a kan man da ake amfani da shi a Najeriya, dalilan hakan kuwa abu ne mai saukin ganewa ga kowa, na farko dai rashin na’urori na aiki, sai fasa-kaurin mai ta kan iyakoki, sannan kuma ayyukan sauran sassan kamfanin ba shi da ingancin da zai iya ba mu tabbacin adadin mai da aka yi amfani da shi a cikin kasa. Yana dai ba mu yawan man da aka fitar daga ma’ajiya wato Depo biyo bayan sanin adadin motocin da aka yi wa lodi, amma kuma suna fita babu wanda zai iya cankar inda aka yi da mai.”

Mr. Mele Kyari ya ci gaba da cewa, tun lokacin da dokar masana’antar mai ta soke batun biyan tallafin a ran 17 ga watan Faburairun shekara ta 2022, gwamnati ta yanke shawarar samar da kwarya-kwaryar kasafin kudi da zai cike gibin da aka samu har zuwa 30 ga watan Yuni na shekara ta 2023, amma tun daga shekara ta 2022 zuwa 29 ga watan Mayun shekara ta 2023, babu ko da sisin kwabo da aka baiwa kamfanin na NNPC da sunan tallafin mai, wannan ya nuna cewa dukkan dawainiyar ta dawo kan kamfanin, kuma muddin shugaban kasa bai kawowa kamfanin dauki ba, tabbas zai iya fadawa cikin matsaloli na rashin kudi. (Garba Abdullahi Bagwai)