logo

HAUSA

Najeriya ta ba da sanarwar hasashen ambaliya saboda sakin ruwa daga madatsar ruwan Lagdo na Kamaru

2023-10-09 10:48:58 CMG Hausa

Hukumomin Najeriya sun fitar da sanarwar hasashen ambaliya ga wasu jihohi a fadin kasar biyo bayan sakin ruwa daga madatsar ruwan Lagdo na kasar Kamaru.

A kalla jihohi tara a Najeriya, wadanda ke da al’ummomi a gabar kogin Benue, za su iya fuskantar matsalar sakin ruwan da ake sa ran zai kai har zuwa karshen watan Oktoba, kamar yadda Mustapha Ahmed, shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA ya shaida wa manema labarai a Abuja, babban birnin kasar a ranar Asabar.

Sakin ruwa daga madatsar Lagdo ya kasance abin damuwa na tsawon lokaci a Najeriya, inda hakan ke haifar da tumbatsar kogin Benue da ya ratsa jihohin Najeriya da dama da suka hada da Adamawa da Taraba a yankin arewa maso gabas da kuma jihar Benue da jihar Kogi a yankin tsakiyar kasar.

Ahmed ya ce, sakin ruwa da aka yi a baya-bayan nan ya riga ya tarwatsa al’ummar wasu kauyuka kuma hakan na iya haifar da kara lalata amfanin gona da sauran ababen more rayuwa. (Muhammed Yahaya)