logo

HAUSA

NUT: A kalla sama da malamai 300 ne a arewa maso gabashin Najeriya 'yan ta'adda suka hallaka

2023-10-06 16:12:54 CMG Hausa

Kungiyar Malaman makaranta ta Najeriya(NUT) ta tabbatar da cewa sama da `ya`yanta 300 ne `yan kungiyar Boko Haram suka hallaka, yayin da kuma wasu da dama ciki har da dalibai suke hannun masu garkuwa da mutane a jahohin dake arewa maso gabashin Najeriya.

Shugaban kungiyar malamai ta kasa reshen jihar Jigawa Kwamared Abdulkadir Yunusa ne ya tabbatar da hakan lokacin da yake ganawa da manema labarai yayin bikin ranar malamai ta duniya na 2023 wanda aka gudanar a babban filin taro na tunawa da malam Aminu Kano dake birnin Dutse, yace akwai bukatar gwamnatoci a Najeriya su debi sabbin malamai domin cike gibin wadanda suka mutu ko kuma ritaya.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Kungiyar Kwadago ta duniya tare da hukumar UNESCO ne suka kebe kowacce ranar biyar ga watan Oktoba domin gudanar da wannan biki.

Kungiyoyin malamai na jahohin Najeriya cikin har da birnin Abuja sun gudanar da wannan biki a jiya alhamis.

Taken bikin na bana dai shine “Malaman da muke bukata a irin wannan lokaci”

Shugaban kungiyar malamai reshen jihar Jigawa ya ci gaba da zayyano kalubalen da tsarin koyarwa yake fuskanta a jihar Jigawa da ma kasa baki daya.

“ A 2015 muna da malaman makaranta masu koyarwa a cikin aji sun kai dubu 30 a jihar Jigawa a kanana da manyan makarantun sakandare, amma yanzu malaman da muke da su a jihar jigawa ba su fi mutum dubu 16 ba, ka ga kusan fiye da rabi sun sauka kuma makarantu sun karu da yawa, da makarantu 1,900 ne da wani abu, yanzu makarantu 3,400 da wani abu ne, kuma malamai dubu 14-16 su suke bin wadannan makarantun, amma a da makarantu 1,900 malamai dubu 28 ne suke shiga cikin ajujuwan, matsalar tsaro tana daya daga cikin abun dake tsorata malaman makaranta har gobe, mun rasa malamai a arewa maso gabashin Najeriya har sama da mutum 300 wanda `yan boko haram suka kashe, haka yanzu muna da malaman makaranta da yawa da dalibai a tsakiyar Najeriya wanda har yanzu suna hannun `yan ta`adda ba a samu `yan fanso su ba, to wannan ba karamin dagawa kungiyar malaman makaranta hankali yake yi ba a ku san kowanne lokaci muka samu kan mu, shi ya sa kullum muke kira ga gwamnati a fito da matakai wanda za a shawo kan hare-haren `yan ta`adda da yake damun arewacin Najeriya domin ingantuwar ilimin yaran mu”.(Garba Abdullahi Bagwai)