logo

HAUSA

Mamakon ruwan sama ya yi sanadin rasa rai tare da rushewar sama da gidaje 100 a jihar Gombe

2023-10-04 15:40:24 CMG Hausa

Hukumomin bayar da agaji a jihar Gombe dake arewa maso gabashin Najeriya sun tabbatar da mutuwar wani mutum guda yayin da kuma sama da mutane 100 sun rasa muhallan su sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a unguwar Hayin Kwarin Misau dake yankin karamar hukumar Akko.

Mamakon ruwan sama na tsawon awanni biyu ya afku ne a daren Lahadin makon jiya, amma sai a jiya Talata ne 3 ga wata hukumomin suka kammala kiyasta adadin asarar da akayi.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Yanzu haka dai gwamnatin jihar Gombe ta hannun hukumar bayar da agaji ta jihar na tsare tsaren samar da matsuguni ga wadanda annobar ta shafa, ko da yake dai da yawa daga cikin magidanta sun samu mafaka a gidajen `yan uwa da abokan arziki.

Ga dai ta bakin wasu daga cikin wanda iftila`in ya shafa.

“Muna cikin gidajen mu sai ruwa ya fara shigowa, sai muka fara debewa da kofuna da bahuna muna zubarwa ba tare da sanin ruwan ya fi karfinmu ba, daga karshe sai muka ga gidaje sai rushewa suke yi shi ne muka fara fita da matanmu da `ya`yan mu”

“Gidajen mu ne na halak din mu amma yanzu mun kasa shiga, ga mata ga `ya `ya ga mazajen mu amma mun rasa ina zamu je”

“Suna na Jummai uwar marayu, ina tare da marayu na dan kankanen lokaci muna zaune a cikin gida kafin mu Ankara ruwa ya cinye mana dakuna sun rushe mun tsinci kan mu a gindin bishiya da ni da `ya `yana”

Alhaji Abubakar Baranbo shi ne mukaddashin shugaban karamar hukumar Akko, inda yace aikin agajin yafi karfin karamar hukuma.

“Wannan wurin gaskiyar Magana idan ba gwamantin tarayyar ba ta hada karfi da jiha, ba abun da za a iya yi ina gani, sai dai kawai a dan tallafawa mutane kafin kuma mu je mu zauna da gwamantin jiha mu ga yadda za a yi, daman dai gwamna ya ji labari har ma ya turo da wakilan sa karkashin hukumar agajin gaggawa ta jihar.”

Da ma dai hukumar hasashen yanayi ta tarayyar Najeriya ta saka jihar Gombe a cikin jerin jahohin sama da 20 da ake tunanin za su iya fuskantar matsalar annobar ruwan sama a damunan bana.(Garba Abdullahi Bagwai)