logo

HAUSA

Karar Mahamadou Issoufou a kotun CPI kan laifin keta hakkin dan adam da yayata ta’addanci

2023-10-04 17:02:29 CMG Hausa

A jamhuriyar Nijar, tun bayan juyin mulkin da aka yi fiye da watanni biyu, ‘yan Nijar sun fara bayyana fatansu domin ganin an fara gurfanar da tsoffin shugabannin kasar da suka yi mulkin kasar a tsawon shekaru da suka gabata. Wata kungiyar M62 ta bayyana fatanta na kai tsohon shugaban kasar Mahamadou Issoufou gaban kotun hukunta manyan laifufuka ta kasa da kasa.

Daga birnin Yamai, abokin aikimu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

Kungiyar farar hula ta M62 ta ajiye a ranar jiya Talata 3 ga wata a ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar Nijar da wata bukatar tuntubar kotun hukunta manyan laifufuka ta kasa da kasa ta CPI domin kai karar tsohon shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou da sauran mutane kan laifuffukan keta hakkin dan adam da ruruta wutar ta’addanci, da kama mutane da tura su gidan wakafi ba tare da girmama dokoki da ‘yancin kasa da kasa na dan adam ba.

A yanzu dai, ‘yan Nijar sun zura ido suna jiran abin da zai biyo baya game da wannan kara kan Mahamadou Issoufou a gaban kotun CPI, har yanzu dai tsohon shugaban kasar bai ce kome ba game da wannan kara ta kungiyar M62, koda ta bakin lauyoyinsa .

Mamane Ada, sashen Hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar