logo

HAUSA

Gwamantin jihar Taraba zata sake bude kofa ga masu saka jari kan sha`anin noman ganyen shayi da sauran albarkatu.

2023-10-03 15:58:34 CMG Hausa

Gwamnatin jihar Taraba dake arewa maso gabashin Najeriya tace a shirye take ta sake samar da kyakkyawan yanayi ga masu saka jari `yan kasa da na kasashen ketare wajen noma ganyen shayi da sauran tsirrai  masu daraja.

Gwamnan jihar Mr. Agbu Kefas ne ya tabbatar da haka yayin wani jawabi da ya gabatarwa al`ummar jihar a karshen mako a wani bangare na bikin cikar Najeriya shekaru 63 da samun `yanci, yace jihar Taraba jiha ce mai albarkar kasa da ake iya noma mahimman tsirrai da manyan masana`antun sarrafa kayan gona na duniya ke mutukar bukata.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Gwmanan jihar ta Taraba ya ci gaba da cewa yankin Mambila mai dausauyi wanda yake makwaftaka da Jamhuriyar Kamaru yayi fice wajen noman kayayyakin shayi nau’ika daban daban wanda yake iya samar da wani kaso na adadin albarkatun da kamfanonin samar da ganyen shayi na duniya ke amfani da shi.

Yace yanzu haka akwai kadada mai yawan gaske na filin noman irin wadannan albarkatu da masu saka jari ‘yan kasashen wajen ke nomawa a yankin, a don haka gwamnatin jihar ba zata taba yin kasa a gwiwa ba wajen samar da dukkan abubuwan da ake nema don habaka sha`anin noma a jihar .

“Ina tabbatar maku da cewa zamu kawo juyin juya hali a bangaren noma ta hanyar samar da kayayyakin noma na zamani, domin yin hakan zai habaka batun samar da aikin yi da kuma bunkasa samar da wadataccen abinci, tare da hadin kanku za mu mayar da jihar Taraba cibiyar noma a kasa baki daya”

Gwamnan haka kuma yace baya ga bunkasa sha`anin noma, batun ilimi da kiwon lafiya da tsaro da sauran bangarorin tattalin arziki zasu samu kulawa mai kyau, a inda ya yi alkawarin tabbatar da samar da ilimin firamare da na sakandare kyauta kuma dole ga duk wani yaro dan asalin jihar.

Da yake magana kuma kan sha`anin yawon bude idanu gwamna Kefas yace,“Taraba ta kasance cibiyar tattalin arziki mai fafutukar janyo hakulan masu saka jari a fagen yawon bude idanu, kuma zamu kara bude kofofin mu ga duniya”.(Garba Abdullahi Bagwai)