logo

HAUSA

Nijer ta amince Algeria ta shiga tsakani game da rikicin siyasar kasar

2023-10-03 16:16:51 CMG

Kasar Nijer ta amince da shawarar kasar Algeria ta shiga tsakani da nufin lalubo mafitar siyasa game da rikicin kasar ta yammacin Afrika.

Ma’aikatar harkokin wajen Algeria ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar jiya Litinin.

Bayan amincewar Nijer, shugaban kasar Algeria Abdelmadjid Tebboune, ya ba ministan harkokin wajen kasar umurnin ziyartar Niamey, babban birnin Niger, domin fara tattaunawar share fage da dukkan bangarori masu ruwa da tsaki.

Ministan harkokin wajen Algeria Ahmed Attaf, ya bayyana a karshen watan Agusta cewa, kasarsa ta gabatar da mafita a siyasance da zata warware rikicin makwabciyarta Nijer. Kuma manufar ita ce, bayar da wa’adin watanni 6 na tsarawa da aiwatar da mafitar siyasa da zata tabbatar da mayar da kundin tsarin mulkin kasar da ma shugabanci na demokuradiyya. (Fa’iza Mustapha)