logo

HAUSA

Ministan harkokin waje da bangaren sojan Nijar ya nada ya gabatar da jawabin da ya yi shirin gabatarwa a taron MDD karo na 78 a dandalin gwagwarmayya

2023-10-02 18:05:53 CMG Hausa

A ranar jiya Lahadi 1 ga watan Oktoban shekarar 2023, bayan ya dawo daga babban taron MDD karo na 78 da aka kammala a makon da ya wuce, ministan harkokin wajen da bangaren sojan Nijar ya nada, Bakary Yaou Sangare ya gabatar da jawabin da da ya yi shirin gabatarwa a zauren MDD.

Daga birnin Yamai abokin aikinmu, Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

 

Al’ummar birnin Yamai da kewaye sun jima suna dakon wannan babban jawabin da ministan harkokin wajen kasar Nijar, Bakary Yaou Sangare a nan dandalin gwagwarmaya na rond-point Escadrille da ke kusa da sansanin sojojin Faransa, bayan ya fito daga babban taron MDD karo na 78 da ya gudana a birnin New-York na Amurka a makon da ya gabata. A gaban dubun dubatar mutane ne, ministan harkokin wajen Nijar ya gabatar da jawabin da ya kamata ya gabatar da sunan Nijar amma shugabannin MDD suka hana bisa hujjar cewa kasar ta Nijar ta je birnin New-York da tawagogi biyu, inda a cewar sabbin hukumomin Nijar, Faransa nada hannu kan wannan lamarin dalilin ke nan tun dawowarsa a birnin Yamai, shugabannin kwamitin ceton kasa na CNSP suka ga ya dace jawabin Nijar da aka hana a zauren MDD an yi shi a nan dandalin gwagwarmaya na rond-point Escadrille. Kuma kwalliya ta biya kudin sabulu a cewar mambobin CNSP da gwamnatin rikon kwarya, domin sauraren jawabin Bakary Yaou Sangare ya jinjinawa ‘yan Nijar bisa tsayin dakan da suka yi na kare ‘yancinsu da ‘yancin kasarsu duk da matsin lambar kungiyar CEDEAO da kasar Faransa, haka kuma a cikin jawabinsa mista Bakary Yaou Sangare ya bayyana dalilan da suka sa aka ki baiwa Nijar magana a zauren MDD, inda ya zargi shugaban MDD Antonio Guetteres da hada kai da Faransa da wasu kasashen kungiyar CEDEAO biyu domin ganin an hana kasar Nijar gabatar da jawabinta wanda a cikinsa ta nemi ta nuna makircin kasar Faransa cikin harkokin cikin gida na Nijar da kuma yadda kasar ta Emmanuel Macron take da hannu kan tabarbarewar tsaro a kasashen Mali, Burkina Faso da kuma Nijar.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.