logo

HAUSA

AU ta yi kira da kara zurfafa dangantakar dake tsakanin kasashen Afirka da Sin

2023-09-30 16:03:35 CMG Hausa

Mataimakiyar shugaban kwamitin hukumar Tarayyar Afrika AU Monique Nsanzabaganwa, ta yi kira da a kara zurfafa dangantakar dake tsakanin kasashen Afirka da Sin a fannoni daban-daban.

Babbar Jami’ar ta AU ta bayyana hakan ne yayin bikin cika shekaru 74 da kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin a daren Talatar da ta gabata a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.

Nsanzabaganwa ta ci gaba da cewa, kungiyar AU za ta ci gaba da nuna godiya ga kasar Sin wajen aiwatar da shirin raya kasa da kasa, wanda ta ce ya dace da tsarin raya nahiyar Afirka na tsawon shekaru 50, wato ajandar 2063, da kuma ajandar neman ci gaba mai dorewa kafin shekarar 2030 ta MDD.

Ta ce, kungiyar AU tana maraba da irin goyon baya da dama da kasashen Afirka suke bayarwa wajen aiwatar da shirin raya kasa da kasa, kana ta yabawa gwamnatin kasar Sin bisa goyon bayan da take baiwa shirye-shirye daban-daban da kungiyar tarayyar Afrika da kasashen Afirka mambobinta ke aiwatarwa.

A yayin bikin, He Youlin, jami'in kula da ofishin jakadancin kasar Sin a kungiyar AU, ya yi tsokaci kan ra'ayin Nsanzabaganwa, yayin da ya yi kira da a kara karfafa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da AU, musamman dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka. (Yahaya)