logo

HAUSA

Sin ta yi kira ga kasashen duniya su mara baya ga cimma zaman lafiya da tsaro a Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo

2023-09-29 16:56:08 CMG

Mataimakin wakilin kasar Sin na dindin-din a MDD Dai Bing, ya ce kwanciyar hankalin yankin gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, na da alaka da daukacin tsaron yankin manyan tabkuna, yana mai kira ga kasashen duniya su mara baya ga yunkurin tabbatar da kwanciyar hankali da tsaro a yankin gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

Dai Bing ya bayyana haka ne yayin taron Kwmaitin Sulhu na MDD kan nazarin batun Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, inda ya ce kasar Sin na goyon bayan yunkurin da gwamnatin kasar ta yi na shirya babban zabe. Ya ce a baya-bayan nan, takaddamar siyasa ta karu, don haka Sin na fatan dukkan bangarori za su karfafa tattaunawa da warware sabani da tabbatar da cewa, zabe ya gudana cikin lumana kuma bisa muradun kasar da al’ummarta.

A cewarsa, babban zaben a bana, batun ne mai muhimmanci na cikin gidan kasar, kuma Sin na fata kasashen duniya za su girmama cikakken ‘yanci na kasar ta Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, tare da kaucewa tsoma baki da matsin lamba. (Fa’iza Mustapha)