logo

HAUSA

Rukunin Kamfanin Media Trust zai hada karfi da kamfanin dillacin labarum kasar Sin Xinhua wajen bayar da horo

2023-09-29 12:04:26 CMG Hausa

Babban rukunin kamfanin yada labarai na Media Trust mamallakin jaridar DailyTrust da TrustTv da kuma Trust FM ya amince da yin aiki tare da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua wajen horas da ma`aikata da musayar shirye-shiryen video da muryoyi da kuma hotuna.

Hukumomin biyu sun amince da kulla wannan alaka ce lokacin da jagororin kamfanin dillacin labarum kasar Sin Xinhua suka ziyarci hedikwatar kamfanin labarai na Media Trust dake birnin Abuja, dukkannin bangarorin sun tabbatar dacewa alakar tasu zata mutunta dokokin kasa da kasa a fagen sha`anin yada labarai.

Daga tarayyar Najeriya wakilin m Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Da yake gabatar da jawabin sa yayin ziyarar jagoran wakilan kuma mataimakin daraktan kamfanin dillacin labarai na Xinhua mai lura da shiyyar Afrika Mr Li Wenfei yace daman dai akwai dadaddiyar alaka dake tsakanin su da kamfanin MediaTrust amma wannan ziyara zata bayar da dama sabunta alakar ta yadda zata kara karfafuwa tare da shigo da wasu sabbin bukatu da zasu amfani kowanne bangare.

“Wannan kamfani na MediaTrust yana da yarjejeniyoyi da dama da kamfanin dillacin labaru na Xinhua, na jagoranci tawaga ta zuwa wannan waje domin gudanar da taro da shugabannin wannan kamfani don tattaunawa akan abubuwa da zasu kai mu ga cin moriyar juna ta hanyar musayar shirye shiryen rediyo da talabijin, yanzu kamfanin dillacin labaru na Xinhua yana yada shirye shirye ta kafar talabijin baya ga hotuna, kuma ina farin cikin gabatar da bukatar kawo maku  irin shirye-shiryen mu wadanda suka dace da al`adun `yan Najeriya domin amfani dashi”

A jawabin sa babban daraktan sashen labarai da harkokin fasaha na kamfanin MediaTrust Naziru Mika`ilu yace babu shakka kamfanin ya ci gajiya sosai da yin mu`amulla da kamfanin dillacin labaru na Xinhua shekaru da dama da suka gabata, amma duk da haka.

“Akwai wasu bangarorin da dama da muke tunanin bi domin kara karfafa alakar mu, munji dadin cewa kamfanin na Xinhua ya fadada ayyukan su zuwa sauran bangarorin yada labarai baya ga rubutu da hotuna yanzu yana isar da sako ta kafar bidiyo da muryoyi”. (Garba Abdullahi Bagwai)