logo

HAUSA

Sudan ta Kudu ta yaba da dangantakar dake tsakaninta da Sin

2023-09-27 10:55:20 CMG Hausa

A jiya ne, ofishin jakadancin Sin dake Sudan ta Kudu ya yi bikin cika shekaru 74 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin (PRC).
A yayin taron da aka gudanar a Juba, babban birnin Sudan ta Kudu, ministan kula da harkokin shugaban Sudan ta Kudu Barnaba Marial Benjamin, ya yi kira da a gina al'ummar duniya mai kyakkyawar makoma. Yana mai jaddada cewa, duniya na bukatar hadin gwiwa fiye da kowane lokaci, don ciyar da dukkan bil-adama gaba yadda ya kamata.

Benjamin ya yabawa gwamnatin kasar Sin, bisa taimakon da ta bayar, wanda ya kai ga kammala kashin farko na aikin fadada asibitin koyarwa na Juba da ma zamanintar da shi cikin nasara. Ya kuma nuna jin dadinsa ga irin gudummawar da tawagogin likitoci daban daban na kasar Sin suka bayar, ga fannin kiwon lafiya na kasar, tun bayan samun ’yancin kanta a shekarar 2011 zuwa wannan lokaci.
A nasa bangare kuwa, jakadan kasar Sin dake Sudan ta Kudu Ma Qiang ya bayyana cewa, kasashen Sin da Sudan ta kudu, sun tabbatar da amincewa da juna ta fuskar siyasa. Kuma a ko da yaushe, kasar Sin na mutunta ’yancin kan kasar Sudan ta Kudu, kana tana adawa da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar, ta kuma goyi bayan Sudan ta Kudu a lokuta daban-daban, kamar kwamitin sulhu na MDD, tana kuma goyon bayan shirin kasar na tabbatar da zaman lafiya bisa ayyuka na zahiri. (Ibrahim Yaya)