logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta gina madatsun ruwa guda 260 a sassa daban daban na kasar

2023-09-27 09:45:17 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce, ta samu nasarar gina madatsun ruwa har 260 a sassa daban daban na kasar duk dacewa suna fuskantar barazana daga gurbatar muhalli sakamakon ayyukan masana’antu da kuma hada-hadar jama’ar dake zaune a bakin kogunan.

Ministan albarkatun ruwa da tsaftar muhalli Farfesa Joseph Utsev ne ya tabbatar da hakan jiya Talata 26 ga wata yayin bikin Ranar Koguna ta duniya da aka gudanar a birnin Abuja.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.