logo

HAUSA

An kame mutum 20 da ake zargin masu garkuwar da mutane a jihar Taraba

2023-09-25 10:02:24 CMG HAUSA

 

Rundunar ’yan sanda a jihar Taraba dake arewa maso gabashin Najeriya ta sanar da kame mutum 20 da ake zargi da lafin yin garkuwa da mutane da kuma kai hare-hare ga wasu al’umomi a jihar.

A lokacin da yake gabatar da mutanen da ake zargi gaban manema labarai a garin Jalingo, fadar gwamnatin jihar, kakakin rundunar SP Usman Abdullahi ya ce, wannan nasara daya ne daga cikin nasarorin da jami’an tsaro a jihar ke samu wajen kawo karshen ayyukan ’yan ta’adda a jihar baki daya.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.