logo

HAUSA

CNSP da gwamnatin Nijar sun yi walladai da halayyar Antonio Guterres da Faransa kan halartar Nijar a zaman taron MDD karo na 78

2023-09-24 17:55:47 CMG Hausa

A lokacin da kasashen duniya suke halartar babban zaman taron MDD karo na 78 a birnin New-York na Amurka, kasar Nijar da ke halartar taron ta bayyana rashin jin dadinta game da yadda aka hana shugaban diplomasiyar Nijar yin jawabi a zauren MDD. Kwamitin ceton kasa na CNSP ya bayyana bacin ransa a cikin wata sanarwa.

Daga Yamai, abokin aikin mu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

Maganar ta fara bayyana tun a ranar 22 ga watan Satumba amma ta tabbata a hukumance a ranar 23 ga watan Satumba, inda kwamitin ceton kasa na CNSP da gwamnatin jamhuriyar Nijar a cikin wata sanarwa suka dauki al’ummar Nijar da kuma gamayyar kasa da kasa a matsayin masu shaidu game da rashin mutuntawa na sakatare janar na MDD, Antonio Guterres kan manufarsa na kokarin mai da hannun agogo baya game da fita daga rikicin kasar mu Nijar, inji kakakin CNSP. Hakika tare da makircin Faransa da wasu shugabannin kasashe renon Faransa biyu da ke cikin kungiyar CEDEAO, sakatare janar na MDD ya ratse daga aikin da aka dora masa na kawo tarnakaki ga halartar Nijar yadda ya kamata game zaman taron MDD karo na 78, tare da take kundin MDD, game da abin da ya shafi Faransa ta Macron, tana nema ba tare da cin nasara kan kokarinta na mai da gwamnatin Nijar saniyar ware game da tsarin mulkin mallaka da Faransa ta kafa a Nijar tare da hadin kan munafukan kasa na gwamnatin da aka hambarar, da kuma shirin kawo shaidu na zahiri na goyon bayan kasar Faransa da take baiwa kungiyoyin ta’addanci a kai a kai da ke kawo barazana ga tsaron kasar Nijar da kuma daukacin yankin Sahel.  Zuwa ga Guterres, abu ne na kawo goyon baya ga abokansa na kungiyar gurguzancin duniya wannan tare matsin lambar Faransa da kuma tarayyar Turai na hukunta dole dole Nijar da al’ummarta bisa ga zabinsu kishin kasarsu gaban kome.  Kuma kome dadewa gaskiya za ta bayyana, inji sanarwar.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.