logo

HAUSA

Gwamnatocin jihohi a arewacin Najeriya na ci gaba da dakatar da sana’ar hakar ma’adanai a yankunansu

2023-09-23 15:18:33 CMG HAUSA

 

Gwamnatin jihar Kebbi dake arewacin Najeriya ta bi sahun sauran jihohi wajen dakatar da sana’ar hakar ma’adanai a yankunanta, a wani mataki na dakile hanyoyin samun kudaden shiga ga ’yan ta`adda.

Sakataren gwamnatin jihar Alhaji Yakubu Bala Tafida ne ya sanar da dokar dakatar da hakar ma’adanan jiya Juma’a 22 ga wata yayin wani taron manema labarai. Ya ce, bayan nazarin da gwamnati ta yi ta lura akwai daruruwan mutane da suke hakar ma’adanai a jihar ba tare da sanin mahukunta ba.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.