logo

HAUSA

Shugaban 'yan sandan Sin ya gana da baki daga kasashen Afirka ta Kudu, da Suriname, da Najeriya, da Pakistan

2023-09-22 10:15:18 CMG Hausa

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan tsaron jama'a, Wang Xiaohong ya gana da baki daga kasashen Afirka ta Kudu, da Suriname, da Najeriya da Pakistan, wadanda suka zo kasar Sin, don halartar taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar tsaron jama'a na duniya na shekarar 2023 a birnin Lianyungang na lardin Jiangsu dake yankin gabashin kasar Sin jiya Alhamis.

Yayin ganawarsa da Kayode Egbetokun, babban sufeton 'yan sandan Najeriya, Wang ya bayyana cewa, kasar Sin na son yin aiki tare da Najeriya, wajen aiwatar da muhimmin ra'ayoyi da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da karfafa mu'amalar jami'ai, da tsara hanyoyin karfafa matakai, da murkushe laifuffukan da ake aikatawa kan al’ummomin kasashen Sin da Najeriya, da kara yin hadin gwiwa a fannin bincike, da bin diddigin wadanda suka aikata laifi suka arce daga kasar, da tabbatar da doka da oda, da ciyar da hadin gwiwar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Najeriya zuwa wani mataki mai zurfi 

A nasa bangare, Egbetokun ya bayyana aniyarsa ta aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin ƙasashen biyu yadda ya kamata, da zurfafa hadin gwiwa a fannin tsaro da aiwatar da doka. (Ibrahim Yaya)