logo

HAUSA

Kwararru a Afirka sun ce kiwon lafiyar jama’a na cikin hadari yayin da ake fama da matsalar sauyin yanayi

2023-09-20 11:27:02 CMG Hausa

Raunin tsarin kiwon lafiyar jama’a ya yi muni yayin da ake fuskantar matsalolin gaggawa na sauyin yanayi kamar ambaliyar ruwa, gurbacewar yanayi, da saurin yaduwar kwayoyin cututtuka, a cewar masana a taron tattaunawa da aka gudanar ta kafar bidiyo a ranar Talata a Nairobi, babban birnin kasar Kenya.

Brama Kone, jami'in fasaha mai kula da sauyin yanayi da kiwon lafiya a ofishin shiyyar Afirka na Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ya yi nuni da cewa, hauhawar yanayin zafi ya kawo cikas ga kokarin rage cututtuka a nahiyar.

Kone ya ce, gaggauta aiwatar da sakamakon da aka amince da shi a taron sauyin yanayi na Afirka da aka gudanar a Nairobi tsakanin ranar 4 zuwa 6 ga watan Satumba, na da matukar muhimmanci wajen karfafa tsarin kula da lafiyar al'umma a nahiyar yayin da ake fuskantar bala’o’in sauyin yanayi.

Bugu da kari, Kone ya bukaci gwamnatocin kasashen Afirka da su daidaita ayyukan sauyin yanayi tare da kokarin kawar da cututtuka masu yaduwa kamar zazzabin cizon sauro da ke yaduwa zuwa wasu yankuna saboda sauyin yanayi. (Yahaya)