logo

HAUSA

Jam’iyyar PNDS-Tarayya ta bi sahun ’yan Nijar domin yin watsi da matakin soja tare da bayyana matsayinta na sulhunta rikicin Nijar cikin ruwan sanyi

2023-09-18 09:51:40 CMG Hausa

Bayan fiye da wata guda da juyin mulkin da ya tafi da shugaba Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yulin shekarar 2023, tsofuwar jam’iyya mai mulki PNDS-TARAYYA ta fitar da wata sanarwa bisa halin da kasar Nijar take ciki a ranar 15 zuwa 16 ga watan Satumban shekarar 2023. Sanar da ’yan Nijar suka jima suna dako.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya turo mana da rahoto:

Ita dai wannan sanarwa ta biyo bayan wani zaman taron kusoshin jam’iyyar PNDS-TARAYYA daga ranar 12 zuwa 14 ga watan Satumban shekarar 2023. Sanarwar na mai cewa tun ranar 26 ga watan Yulin shekarar 2023, Nijar ta shiga wani hali mai tsanani da sarkakiya, wanda domin fuskantarsa, tsofuwar jam’iyya mai mulki ta gudanar da jerin ayyuka da suka hada da sanarwar kawancen jam’iyyun siyasa masu rinjaye na MRN a ranar da aka yi juyin mulkin domin yin alla wadai da tsare shugaba Mohamed Bazoum da neman a sake shi, da mai da shi kan mukaminsa. Da zanga-zangar magoya bayan jam’iyyar zuwa fadar shugaban kasa a ranar 26 ga watan Yulin wanda aka tarwatsa da kuma jikkata mutane da dama. Da sanarwar matan tarayya OFT a ranar 27 ga watan Yulin a cibiyar jam’iyyar dake birnin Yamai, wacce a yayinta masu zanga zangar goyon juyin mulki suka farma magoya bayan PNDS Tarayya da duka da kona motoci fiye da 45.

Kusoshin PNDS Tarayyar sun gudanar da kai da kawo domin neman bakin zaren rikicin bisa ga matakan kungiyar CEDEAO da UEMOA na sanyawa Nijar takunkumi tare da yin kiran maida shugaba Bazoum Mohamed kan mukaminsa ba tare da bata lokaci ba. Kungiyar yammacin Afrika ta amince da daukar matakan soja kan sojojin kwamitin ceton kasa na CNSP. Matakin sojan da ya janyo bacin ran ’yan Nijar da ma al’umomin kasashen kungiyar CEDEAO musamman ma a Najeriya. A cewar sanarwar, hakan ya sa an maida jam’iyyar PNDS Tarayya saniyar ware, ganin cewa ba ta bayyana matsayinta bisa ga wannan matakin soja kan Nijar sabanin sauran jam’iyyun siyasa da suka nuna adawarsu. Sai dai muryoyi sun fara tashi domin jam’iyyar ta fito karara ta bayyana matsayinta, ganin cewa wasu jam’iyyun siyasa suna nunawa tsofuwar jam’iyya karen tsana. Dalilin haka ne, bayan tattaunawa kan wannan batu, wani bangare mai rinjaye ya bayyana kin amincewarsa da matakin soja. Jam’iyyar PNDS Tarayya ta jaddada niyyarta na sulhunta rikicin siyasar Nijar bisa sharudan da suka hada da sakin shugaba Mohamed Bazoum da iyalinsa, maido shi bisa mukaminsa na shugaban kasa da tabbatar da tsarin demokaradiya ta kowane hali tare da yin watsi da matakin soja.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.