logo

HAUSA

Shugaban gwamnatin sojan kasar Nijar yayi maraba da sanya hannu kan kafa sabuwar gamayyar kasashen Sahel da ake kira AES

2023-09-17 19:22:24 CMG Hausa

Shugaban gwamnatin sojan jamhuriyar Nijar, birgadiye janar Abdourahamane Tchiani yayi farin cikinsa tare da jinjina ta musamman game da sanya hannu mai cike da tarihi kan kundin Liptako-Gourma a jiya 16 ga wata a birnin Bamako na kasar Mali da ke tabbatar da kafa gamayyar kasashen Sahel (AES) a hukumance.

Daga birnin Yamai, abokin aikin mu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

Ita wannan gamayya da aka kulla tsakanin Mali, Burkina Faso da Nijar, kasahe ‘yan uwan juna kuma abokai na shaida matakin farko na daukar  nauyin tabbatar da tsaro da kuma kare al’umomin mu, inji shugaban rikon kwarya Abdourahamane Tiani.

Shugaban kwamitin ceton kasa na CNSP ya jinjinawa kyaukyawar niyyar Nijar tare da Mali da kuma Burkina Faso cikin wannan muhimmin yaki da annobar ta’addanci, kamar yadda wannan niyya ta tabbata a birnin Bamako.

Ta dalilin wannan huldar dangantaka da aka karfafa cikin kyaukyawan tunanin zumunci da taimakon juna, imani nada girma na mu kai tare ga samun nasarar kawar da barazanar da kasashenmu suke fuskanta.

Allah ya daukaka wannan gamayya da aka kulla a ranar 16 ga watan Satumban shekarar 2023 tsakanin Mali, Burkina Faso da Nijar, tare za mu gina wani yankin Sahel mai cike da ci gaba da kuma hadin kai, inji shugaban CNSP.

Saidai masu fashin baki kan al’amuran siyasar duniya na kallo wannan mataki tamkar aza tunbalin gogayya da kungiyar yammacin Afrika CEDEAO da kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar suke ganinta a matsayin wata kungiyar da ta kasa aikinta na tabbatar da ci gaban shiyyar ta fuskar tattalin arziki da tsaro. Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar