logo

HAUSA

Yin Li ya gana da shugabar majalissar dokokin Angola

2023-09-17 21:12:30 CMG Hausa

Shugabar majalissar dokokin kasar Angola, kuma mamba a ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar jam'iyyar MPLA ta kasar Carolina Cerqueira, ta zanta da babban jami’i a ofishin siyasa, na kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma sakataren kwamitin jami’iyyar kwaminis na birnin Beijing Yin Li.

Jami’an biyu sun gana ne a Juma’a a birnin Luanda fadar mulkin kasar Angola, albarkacin bikin raya al’adu da musayar harkokin yawon bude ido mai taken "Hello, Beijing", wanda ke da nufin taimakawa mazauna birnin na Luanda, kara fahimtar muhimman abubuwan tarihi da na al’adun birnin Beijing, a matsayin sa na shahararren birni a kasar Sin.   (Saminu Alhassan)