logo

HAUSA

Tashar sararin samaniya ta Sin ta nuna zane-zane guda 10 da matasan kasashen Afirka suka zana

2023-09-17 16:21:08 CMG Hausa

Kwanan baya, an gudanar da shiri mai lakabin “Mafarkina na shiga sararin samaniya: ‘yan sama jannatin kasar Sin su yi mu’ammala da matasan kasashen Afirka ta bidiyo”, tare da gudanar da bikin bayar da lambobin yabo na gasar zane-zane a birnin Beijing da sauran wurare 8 dake kasashen Afirka. 

Yan sama jannatin kumbon Shenzhou-16 dake cikin tashar sararin samaniya ta Sin, sun nuna, da kuma bayyana zane-zane guda 10 da matasan kasashen Afirka suka zana, kuma aka aike da su sararin samaniya zuwa tashar ta Sin.

A watan Maris na shekarar bana, kwamitin aiwatar da matakan dake biyo bayan dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, da ofishin kula da harkokin zirga-zirgar sararin samaniya dake dauke da ‘yan sama jannati na kasar Sin, sun gudanar da gasar zane-zane mai taken “Mafarkina” ga matasan kasashen Afirka, gasar da ta jawo hankulan matasan kasashen Afirka fiye da 2000 har suka shiga cikinta. 

A karshe dai, zane-zanen da matasan guda 10 suka gabatar, sun sami lambar yabo ta “Tianhe”, wato an nada masa sunan babban kumbon tashar sararin samaniya ta Sin, kuma zane-zanen sun shiga tashar sararin samaniya ta “Tiangong”, tare da kumbon Shenzhou-16 dake dauke da ‘yan sama jannati.

Yayin shugaban sashen Afirka na ma’aikatar harkokin wajen Sin Wu Peng yake hallartar bikin, ya ba da jawabin cewa, wannan ne karo na farko da tashar sararin samaniya ta Sin ta gudanar da baje kolin zane-zane na kasa da kasa, wanda ya shaida zane-zanen dake dauke da “mafarkin Afirka”, da suka shiga sararin samaniya mai fadi. 

Ya ce wannan shiri na “mafarkan Afirka na shiga sararin samaniya”, babban sakamako ne da hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka ya samu a cikin sabon zamani, kuma ya shaida sakamakon ci gaba, da damammaki da Sin ta raba wa kasashen Afirka a cikin dogon lokaci. (Safiyah Ma)