logo

HAUSA

Shugaban Najeriya ya sha alwashin zurfafa harkokin diflomasiyya a taron UNGA

2023-09-16 16:07:50 CMG Hausa

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana manufar zurfafa diflomasiyyarsa ta fuskar tattalin arziki, a yayin da zai halarci babban taron MDD (UNGA) gobe Lahadi.

Ajuri Ngelale, mai magana da yawun shugaban Najeriyar, shi ne ya bayyana hakan lokacin da yake ganawa da manema labarai a Abuja,babban birnin Najeriya. Yana mai cewa, ganawar da shugaban zai yi da shugabannin ‘yan kasuwa da shugabannin kasashen duniya, a gefen babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78, na daga cikin abubuwan da aka tsara shugaban zai yi.

A yayin ziyarar da zai kai kasar Amurka, shugaba Tinubu zai halarci shirin kasuwanci na Afirka na duniya wato Global Africa Business Initiative, domin nuna karfin Najeriya ga shugabannin ‘yan kasuwan kasa da kasa, da kuma jagorantar taron kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa na kasar.(Ibrahim)