logo

HAUSA

Najeriya da tallafin kungiyoyin lafiya na duniya za su kashe dala buliyan 2 wajen yaki da zazzabin cizon sauro

2023-09-15 08:59:53 CMG Hausa

Ministan kiwon lafiya na tarayyar Najeriya Farfesa Mohammed Ali Pate ya tabbatar da cewa, gwamnatin Najeriya ta himmatu sosai wajen shawo kan matsalolin zazzabin cizon sauro a kasar.

Ya tabbatar da hakan ne lokacin da ya jagoranci wata tawagar kungiyar agajin lafiya ta duniya Global Health Partners zuwa ziyarar ban girma ga gwamnan jihar Kano, ya ce yanzu haka kokarin yaki da wannan cuta ta cizon sauro na kan gaba cikin jerin matsalolin dake ciwo ma’aikatar lafiya ta tarayyar tuwo a kwarya.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Ministan lafiyar na tarayyar Najeriya ya ce, duk da wannan kalubale gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta himmatu sosai wajen inganta dukkan ayyukan da suka shafi kiwon lafiyar al’ummar kasar, wannan ce ma kamar yadda ministan ya fada ya janyo hankulan kungiyoyin agajin lafiya na kasa da kasa wajen samar da tallafin kudade domin aikin hadin gwiwa wajen yaki da cutar zazzabin cizo sauro, da tarin fuka da kuma cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV/AIDS.

Ya ce, a zancen nan da ake yi kungiyar Global Health Partners ta samar da tsabar kudi har dala biliyan 2 a matsayin tallafinta, inda ya ce, za a yi amfani da kudaden ne a wasu jahohi ciki har da jihar Kano.

 “Najeriya ce ke da kaso 30 cikin 100 na kasashen da suke fama da matsalolin cututtuka masu saurin yaduwa a duniya, kuma jihar Kano ita ce jihar da aka fi fuskantar wannan matsala a kasa baki daya. Yana da kyau matuka kyakyawan ayyukan da gwamnatin Kano ta yi a shekarun baya wajen yaki da wasu cututtuka a samu a kara fadada shi ta hanyar yin hadin gwiwa da kungiyoyin lafiya na duniya da muke mu’amulla da su.”

Da yake nasa jawabin, gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya tabbatarwa ministan tare da tawagar kungiyar ta Global Health Partners, cewar a shirye gwamnatin Kano take ta hana karfi da duk wata kungiya da take da manufar kyautata harkokin kiwon lafiyar al`ummar jihar Kano. (Garba Abdullahi Bagwai)