logo

HAUSA

An bude dandalin tattauna hadin gwiwar tattalin arziki na Sin da Aljeriya

2023-09-14 10:09:16 CMG Hausa

Manyan jami’ai da ‘yan kasuwa na kasashen Sin da Aljeriya, sun hallara a birnin Oran na bakin tekun yammacin Aljeriya, domin gudanar da taron tattauna hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.

A jawabin sa yayin taron a jiya Laraba, jakadan Sin a Aljeriya Li Jian, ya ce dandalin na da nufin karfafa hadin gwiwar raya tattalin arziki, da cinikayya tsakanin kasashen biyu, ta hanyar samar da wani fage na ingiza tattaunawa tsakanin ‘yan kasuwar Sin da na Aljeriya.

A nasa bangare kuwa, gwamnan lardin Oran Said Saayoud, ya ce yana maraba da zuwan jarin kasar Sin lardin sa, kuma sabuwar dokar Aljeriya mai nasaba da hada hadar zuba jari, za ta samarwa masu zuba jari na ketare kyakkyawan yanayi na gudanar da harkokin su yadda ya kamata.

Taron wanda ofishin jakadancin Sin dake Aljeriya da gwamnatin lardin Oran suka yi hadin gwiwar shiryawa, ya hallara mutane 200, ciki har da ‘yan majalissar dokokin kasar Aljeriya, da jami’an gwamnatin kasar, da ma ‘yan kasuwa daga kasashen biyu.  (Saminu Alhassan)