logo

HAUSA

’Yan gudun hijira na ci gaba da samun tallafin kayan abinci a jihar Niger

2023-09-14 11:12:47 CMG Hausa

 Hukumar bayar da agajin gaggawa a jihar Niger dake arewa ta tsakiyar Najeriya ta kara fadada shirinta na bayar da tallafin kayan abinci ga dubban ’yan gudun hijira dake zaune a sansanoni daban daban dake manyan biranen jihar.

A farkon wannan makon ne gwamnatin jihar ta Niger karkashin kulawar hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar ta kaddamar da shiri na musamman domin tallafawa rayuwar ’yan gudun hijirar da suka tagaiyara bayan barin muhallan su sakamakon hare-haren ’yan ta’adda da kuma sauran bala’o’i da suke da nasaba da ambaliyar ruwa.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Sama dai da ’yan gudun hijira dubu uku ne suka amfana da wannan tallafi.

Barista Mairo Muhammad ita ce babbar sakatariya a hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Niger,

“Tallafi dai da muka kawo an gani dai shinkafa, wake, gari, manja, man gyada. An kawo ne ga wadanda kaddara ta fada kansu suka zamanto dole su bar wuraren zamansu. Su zamanto suna wani waje tukuna. Har zuwa lokacin da muke fatan Allah zai kawo saukin shi, shi ya sa ake ce masu they have being displaced don an dauke su daga inda suke wata annoba ta faru, sun bar wurin nan, to wannan, to wannan abun da aka kawo dai ya nuna ne cewa shi gwamna ya san da su, shi ya sa bai kirga su cikin kowacce karamar hukuma ba, shi ya sa ya ce a kawo masu wannan tallafi domin su samu sassauci, su kuma san cewa an san suna nan.”

To ko yaya ’yan gudun hijirar suka ji da wannan tallafi?

“Maimuna Sani daga Bunu. Mun samu abinci. Yadda ake zato mu samu shinkafa da wake da mai da magi da garin kwaki, duka an ba mu. In ba don wannnan tallafi ba bara muke yi ko wurin kwanciya ya yi mana wahala.”

Amma dai duk da gamsuwa da suka nuna a kan wannan tallafi, Malama Maimuna ta yi kira ga gwamnati cewa,

“A taimaka mana da wadanann mutane da suka addabe mu a cikin karkara, ga shi mun yi noma a bara sun hana mu diba. Bana ma ga shi sun zo, Taimako muke nema a raba da wadannan mutane, su bar mu mu zauna a garinmu, nan ma da muke zaune mu ba mu ji dadin zaman garin ba sabo da ba mu saba ba, wani lokacin cikin kangaye muke kwana. Abincinmu da dukiyoyinmu, da rayuwar ’ya’yanmu da jikokinmu da manya-manya duka an yi garkuwa da su, ba mu da kudin fanso su. Tun da kudin da suke cewa a hada a kai sun fi karfin mu.” (Garba Abdullahi Bagwai)