logo

HAUSA

Adadin wadanda suka mutu dalilin ambaliyar ruwa a Libya ya haura 5500

2023-09-14 09:59:49 CMG Hausa

Mai kula da ayyukan jin kai ta MDD a Libya Georgette Gagnon, ta nada tawagar gaggawa da za ta tallafawa hukumomin yankin da abokan hulda bayan aukuwar mummunar ambaliyar ruwa hade da guguwar iska da aka yiwa lakabi da Daniel jiya Laraba.

Hukumar kula da ayyukan jin kai ta MDD OCHA ta bayyana cewa, an tura tawagar mutane 12 da aka baiwa aikin tantance bala’o’i da gudanar da ayyukan majalisar a kasar Libya, domin tallafa wa matakan da hukumar za ta dauka dangane da bala'in ambaliyar ruwa da ta hallaka dubban mutane tare da bacewar wasu dubbai. lura da cewa majalisar na amsa kiraye-kirayen da suka shafi taimako da bayar da agaji a yankunan da abin ya shafa.

Jami'an jin kai na majalisar sun ce ana ci gaba da gudanar da ayyukan bincike da ceto a Libya, karkashin jagorancin hukumomin kasa da sojoji da kungiyar agaji ta Red Crescent ta Libya da kuma masu aikin sa kai na cikin gida.

Adadin wadanda suka mutu sakamakon mummunar ambaliyar ruwa da ta afkawa gabashin kasar Libya ya kai 5,500, yayin da wasu 7,000 suka jikkata, kamar yadda wani jami'in kasar ya sanar a ranar Laraba.

Osama Ali, kakakin hukumar ba da agajin gaggawa da ke Tripoli ya ce har yanzu ba a iya tantance adadin wadanda suka mutu ba saboda ana ci gaba da zakulo gawarwaki daga yankunan da lamarin ya shafa. (Yahaya)