logo

HAUSA

Najeriya ta ba da sanarwar gargadin ambaliyar ruwa ga jihohin arewacin kasar

2023-09-13 21:19:49 CMG Hausa

 

Mahukunta a Najeriya, sun fitar da sanarwar gargadin yiwuwar afkuwar ambaliyar ruwa ga jihohi 13 daga cikin jihohi 19 na arewacin kasar, inda suka bukaci da a sanya ido tare da samar da matakan gaggawa domin dakile afkuwar bala’in.

Wata sanarwar da hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar Najeriya (NEMA) ta fitar a jihar Legas da ke kudu maso yammacin kasar, ta bayyana cewa, sanarwar gargadin ta zo ne a matsayin wani mataki na zama cikin shiri, domin dakile matsalar ambaliyar ruwa da kuma tabbatar da tsaron lafiyar al’umma bisa la’akari da mamakon ruwan sama da ake fuskanta a yankin arewacin kasar.

Hukumar ta ce a kalla al’ummomi 50 ne, galibi a yankin arewacin kasar, za su iya fuskantar ruwan sama mai karfin gaske wanda zai iya haifar da ambaliyar ruwa tsakanin ranar 13 da 17 ga watan Satumba.(Ibrahim)