logo

HAUSA

Shugaban Najeriya ya ba da umarnin gudanar da bincike game da yawaitar hadurran jiragen ruwa

2023-09-13 10:22:05 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Tinubu ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike, game da yawaitar asarar rayuka da ake samu sakamakon hadurran jiragen ruwan dakon fasinja a sassan kasar.

Shugaba Tinubu ya umarci sassan hukumomin gwamnati, ciki har da jami’an tsaro, da masu kare hadurra a hanyoyin ruwa da sauran sassan sufuri, da su yi hadin gwiwa, domin gano musabbabin aukuwar matsalar, da ma zakulo dabarun shawo kanta. Kaza lika ya umarci sassa masu ruwa da tsaki da su sake nazari, game da cikakkun matakan dakile hadurran jiragen ruwa, da tabbatar da ana bin dokokin kasar masu nasaba da hakan yadda ya kamata.

Kaza lika, shugaban Najeriyar ya ce umarnin da ya bayyana gudanar da cikakken bincike game da yawaitar hadurran jiragen ruwa a sassan kasar, na shaida aminyarsa, ta tabbatar da cewa hukumomin gwamnati da aka dorawa alhakin kare dokoki, ko dakile aukuwar hadurra, suna sauke dukkanin nauyin dake wuyansa yadda ya kamata. (Saminu Alhassan)