logo

HAUSA

Adadin wadanda suka mutu sakamakon mamakon ruwan sama a Libya ya kai 5300

2023-09-13 14:13:53 CMG Hausa

Akalla mutane 5,300 ne ake ganin sun mutu sakamakon mamakon ruwan sama, kamar yadda ma’aikatar harkokin cikin gida ta gwamnatin gabashin Libya ta shaidawa kamfanin dillancin labaran kasar LANA a ranar Talata.

Kimanin mutane 10,000 ne aka rawaito sun bace, a cewar Tamer Ramadan, shugaban tawagar kungiyar agaji ta Red Cross da Red Crescent a Libya, yayin wani taron manema Labarai a jiya Talata. (Yahaya)