logo

HAUSA

Adadin wadanda suka mutu a girgizar kasar Morocco ya zarce 2,900

2023-09-13 09:50:23 CMG Hausa

Sanarwar baya-bayan nan da gwamnatin Morocco ta fitar a jiya Talata ta ce, adadin wadanda suka mutu a sakamakon mummunar girgizar kasa a kasar ya haura 2,901, yayin da wasu 5,530 suka samu raunuka.

A birinin Ouirgane dake cikin tsaunuka, daya daga cikin kauyukan da girgizar kasar ta fi shafa, ‘yan jaridan kamfanin dillancin labarai na Xinhua sun ga yadda gidaje suka ruguje kuma masu aikin ceto na amfani da motar hakar rami wajen kwashe baraguzan gine-gine.

Morocco ta amince da tayin agaji daga Spaniya, Birtaniya, Hadaddiyar Daular Larabawa da Qatar, yayin da taimako daga wasu kasashe ke jiran amincewa.

Zhang Feigong, shugaban sashen Agadir na tawagar likitocin kasar Sin dake kasar Morocco, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, tawagar likitocin sun ba da gudummawar kayayyakin jinya da ake bukata cikin gaggawa kamar na'urorin gwajin oxygen da na bugun jini,   da man tsabtace hannu na kashe kwayoyin cuta ga asibitocin yankin. (Yahaya)