logo

HAUSA

Sinawa mazauna Morocco sun tattara kudaden tallafi

2023-09-12 10:12:06 CMG Hausa

Sinawa mazauna kasar Morocco, sun samar da tallafin kudade da sauran ababen bukata ga al’ummun kasar da ibtila’in girgizar kasa mai karfi ya auku, wadda kuma kawo yanzu ta haddasa rasuwar mutane kimanin 2,862.

Da yake tsokaci game da hakan, yayin tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a jiya Litinin, shugaban kungiyar Sinawa mamallaka kamfanoni da ‘yan kasuwa dake Morocco Lin Weiqiang, ya ce sun yi kira ga mambobin su da su samar da tallafi yadda ya kamata, kuma da zarar sun tattara, za su mika shi ga ofishin jakadancin Sin dake kasar.

Lin ya ce a halin yanzu ma, cibiyar bunkasa cinikayya ta Sin da Morocco ta fara mika kayayyakin agajin gaggawa zuwa yankunan da ibtila’in ya auku.

Tun a ranar Asabar din karshen makon jiya ne kungiyar Red Cross ta Sin, ta sanar da aniyar mika tallafin kudaden da suka kai dala 200,000 ga kungiyar agaji ta Morocco ko MRC, a matsayin agajin jin kai na gudanar da aikin ceto, da ayyukan rage radadin ibtila’in. (Saminu Alhassan)