logo

HAUSA

Gwamnatin Kano za ta hada karfi da kasar Ghana a bangarorin kiwon lafiya da samar da ababen more rayuwa

2023-09-12 09:35:10 CMG Hausa

 Gwamnatin jihar Kano dake arewacin Najeriya ta sha alwashin hada karfi da ma’aikatar lafiyar kasar Ghana wajen bunkasa sha’anin kiwon lafiya da samar da ababen more rayuwa.

Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ne ya tabbatar da hakan jiya Litinin 11 ga wata, lokacin da yake karbar bakuncin mataimakin ministan lafiya na kasar Ghana Mahama Ase Asesini a gidan gwamnatin jihar, inda ya ce hada karfi da kasar Ghana hakika zai taimaka sosai wajen cimma kudirin gwamnatin Kano na kyautata lafiyar iyali a dukkan matakai.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ce, jihar Kano wadda ta fi kowace jiha a fadin tarayyar Najeriya yawan jama’a, tana fuskantar kalubale da dama musamman ta fuskar kiwon lafiya, samar da ababen more rayuwa, ilimi da kuma ingantuwar yanayin wal-walar al’umma.

A sakamakon hakan ne gwamnan na Kano ya ce, gwamnati ta bude kofofin neman agajin gwamnatoci da kungiyoyin kasa da kasa da za su shigo jihar domin yin aikin hadin gwiwa domin tabbatar da cin moriyar juna.

"Mai girma minista a lokacin da muka shigo gwamnati mu tarar da al’amauran kiwon lafiya a tabarbare, babu wani abu da yake tafiya yadda ya kamata, wannan ta sa muka bullo da wasu manufofi daban daban da za su farfado da harkokin kiwon lafiya a jihar Kano. Manufofin da suka kunshi kula da mata masu juna biyu kyauta a lokacin asibitocinmu, kuma yanzu haka mun yi nisa wajen yin kwaskwarima ga da yawa daga cikin manyan asibitocin dake yankunan kananan hukumomi 8 na cikin kwarya birni."

A lokacin dayake nasa jawabin, mataimakin ministan lafiya na kasar Ghana Mahama Ase ya ce, ya jagoranci wata tawagar jami’an lafiya na kasar Ghana ne zuwa Kano domin nazarin hanyoyin da suke bukatar hadin gwiwa tare da kyautata dangantaka tsakanin Kano da kasar ta Ghana. (Garba Abdullahi Bagwai)