logo

HAUSA

Mutane a kalla 26 sun mutu sanadiyyar hatsarin kwale-kwale a Nijeriya

2023-09-11 09:27:25 CMG Hausa

An gano gawarwaki 26, yayin da wasu mutane 44 suka bace biyo bayan kifewar wani kwale kwale a yankin karamar hukumar Mokwa ta jihar Niger dake tsakiyar Nijeriya.

Hatsarin ya auku ne da misalin karfe 8 na safiyar jiya Lahadi, tsakanin madatsun ruwa na Jabba da Kainji, a yankin Gbajibo na karamar hukumar Mokwa.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Niger (NESMA) ta tabbatar da cewa, sama da mutane 100 ne a cikin kwale-kwalen, wadanda suka fito daga yankunan Gbajibo da Ekwa da Yankyade, kuma suna kan hanyarsu ce ta zuwa gona a daya bangaren kogin Niger, wato tsohon yankin Gbajibo.

Kakakin hukumar NESMA Ibrahim Husseini, ya bayyana cewa, hukumar na hada hannu da jami’an karamar hukumar Mokwa da masu ninkaya, domin gudanar da ayyukan bincike da ceto a wurin da lamarin ya auku. (Fa’iza Mustapha)