logo

HAUSA

Masar ta ce cika kogin Nilu da Habasha ta yi ya saba yarjejeniyar da suka kulla

2023-09-11 10:36:32 CMG Hausa

Masar ta ce matakin Habasha na cika katafariyar madatasar ruwan kasar ba tare da cimma matsaya da kasashen Masar da Sudan da kogin ya ratsa ba, ya take ka’idojin yarjajeniyar da kasashen 3 suka cimma.

A jiya ne firaministan Habasha Abiy Ahmed ya sanar a shafin sada zumunta na X da a baya ake kira da Tweeter cewa, an kammala mataki na 4 kuma na karshe na cike madatsar ruwan.

Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Masar ta fitar a jiyan, ta bayyana matakin na Habasha a matsayin keta ka’idojin yarjejeniyar da kasashen 3 suka cimma a shekarar 2015.

Ma’aikatar ta jaddada cewa, yarjejeniyar ta tanadi cewa, dole ne kasashen 3 su amince da ka’idojin cikawa da yadda za a tafiyar da aikin madatsar ruwan kafin a fara cikawa.

Ta kara da cewa, daukar irin wannan mataki ba tare da tuntubar sauran bangarorin ba, ya raina muradu da hakkokin kasashen biyu da tsaron ruwa, karkashin dokokin kasa da kasa. (Fa’iza Mustapha)