logo

HAUSA

Cibiyar Afirka CDC za ta yi hadin gwiwa da mambobin G20 a fannin kiwon lafiya

2023-09-11 10:16:26 CMG Hausa

Cibiyar kandagarki da shawo kan cututtuka masu yaduwa ta nahiyar Afirka ko Africa CDC, ta sanar da aniyar yin hadin gwiwa da mambobin kungiyar raya tattalin arzikin duniya ta G20, a fannonin da suka jibanci kiwon lafiya.

Africa CDC, kwararriyar hukumar kiwon lafiya dake karkashin kungiyar tarayyar Afirka AU, ta jinjinawa amincewar da aka yiwa AU, ta zama mambar dindindin a G20.

Wata sanarwar da aka fitar game da hakan, ta ce "Wannan mataki ya fayyace matsayin Afirka, na kasancewa muhimmiyar abokiyar ta lafiya a harkokin duniya, wadda ke cikin shirin ba da gudummawa, da maida hankali ga muhimman batutuwan dake jan hankalin nahiyar, wadda ke matsayin mazauni ga yankin ciniki maras shinge mafi girma a duniya."

Kaza lika, sanarwar ta ce, "bisa nauyin dake wuyanta, kana da matsayinta na babbar cibiyar kiwon lafiya ta Afirka, Africa CDC za ta wakilci kasashen nahiyar a taron ministocin kungiyar G20" dake tafe.

Kungiyar AU dai ta ayyana cibiyar Africa CDC a matsayin wakiliya mai karfi dake wakiltar muryar al’ummun Afirka su biliyan 1.4, wadda a yanzu kuma ke tafiya kafada da kafada da kungiyar tarayyar Turai ta EU, a matsayin kungiya ta biyu, mai wakilcin nahiya, da babban yankin kasashe daban daban, wadda kuma ta yi nasarar zama mambar dindindin a kungiyar G20.  (Saminu Alhassan)