logo

HAUSA

Shugaban Hukumar AU Ya Yi Kira Da A Hada Kan Kasashen Nahiyar A Ranar AU

2023-09-10 16:31:48 CMG Hausa

Shugaban hukumar gudanarwar kungiyar Tarayyar Afirka (AU) Moussa Faki Mahamat, ya yi kira ga hadin kan nahiyar, domin yakar tarin kalubalen dake addabarta

Da yake tsokaci game da tashe-tashen hankulan dake faruwa a sassan duniya, Mahamat ya ce, akwai fargabar cewa, nahiyar Afirka za ta iya sake zama wani fage na neman yin fito na fito na babakere.

A don haka, ya yi kira ga hadin kan nahiyar, don magance illar kalubalen da duniya da ma nahiyar ke fama da su kan makomar nahiyar.

Faki ya kuma bayyana cewa, tushen hadin kan nahiyar ya dogara ne kan dimbin wadatar da aka samar, da nufin biyan muhimman bukatun al'ummar nahiyar, ta hanyar hada-hadar tattalin arziki mai dimbin yawa na al'ummar da aka bari a baya."

Daga nan sai ya yi kira da a tabbatar da ajandar ci gaba da dunkulewar nahiyar Afirka kamar yadda aka tsara a cikin ajandar raya nahiyar ta kungiyar AU na shekaru 50 nan da shekarar 2063.(Ibrahim)