logo

HAUSA

Shugaban Majalisar Dinkin Duniya ya nuna alhininsa da asarar rayuka da aka yi a girgizar kasar Morocco

2023-09-09 17:09:43 CMG

Sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya nuna alhininsa game da asarar rayuka da aka yi a girgizar kasa a Morocco, a cewar kakakinsa a ranar Asabar.

Sanarwar ta ce Majalisar Dinkin Duniya a shirye take ta taimaka wa gwamnatin kasar Morocco a kokarinta na taimakawa al'ummar da abin ya shafa.

Girgizar kasa mai karfin awo 6.8 ta afku a kasar Morocco ranar Juma'a da karfe 11:11 na dare agogon cikin gida (2211 GMT) a zurfin kilomita 18.5 a wasu kilomita 70 kudu maso yammacin birnin Marrakesh. Adadin wadanda suka mutu ya karu zuwa 632, kamar yadda kafafen yada labarai na cikin gida suka ruwaito a ranar Asabar. (Yahaya)