logo

HAUSA

Sin na nanata aiwatar da ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD a siyasance

2023-09-08 15:22:01 CMG HAUSA

 

A jiya ne mataimakin zaunannen wakilin Sin dake MDD Geng Shuang ya gabatar da jawabi a gun taron kwamitin sulhu kan batun kiyaye zaman lafiya na MDD, inda ya nanata cewa, ya kamata a nace ga aiwatar da ayyukan kiyaye zaman lafiya da MDD a siyasance.

Geng Shuang ya yi nuni da cewa, ayyukan kiyaye zaman lafiya wani karin mataki ne ga kokarin siyasa da diplomasiyya, kuma mataki ne kawai ba burin da ake sa ran cimmawa ba. Kamata ya yi tawagar musamman ta kiyaye zaman lafiya ta nace ga wannan ka’ida tun lokacin da aka ba ta izni da girke sojoji da gudanar da ayyukanta, kana a tabbatar da cewa, duk ayyukan da tawagar za ta yi goyon baya a kai su kasance bisa matakin diplomasiyya.

Geng Shuang ya kara da cewa, gwamnati da jama’ar kasar da abin da ya shafa, su ne tushen tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwa. Ya kamata, tawagar ta samun amincewa da goyon bayan gwamnatin da jama’arta kafin ta aiwatar da harkokinta, matakin da zai tabbatar da wanzar da zaman lafiya a siyasance. Ficewar tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD daga kasar Mali a baya-bayan nan ya haifar da damuwa daga sassa daban daban, kuma cikas da tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo (DRC) ke fuskanta wajen gudanar da ayyukanta na da matukar damuwa. Ya kamata MDD ta koyi darasi ta inganta ayyukanta na wanzar da zaman lafiya. (Amina Xu)