logo

HAUSA

Kasashen Afirka sun kammala taron sauyin yanayi tare da amincewa da tabbatar da adalci a fannin

2023-09-07 10:09:58 CMG Hausa

Kasashen Afirka sun kammala taron sauyin yanayi na yini uku a birnin Nairobi na kasar Kenya, inda suka fitar da sanarwar kammala taron, mai lakabin “Sanarwar Nairobi”, wadda ke kunshe da ajandar nahiyar game da shawo kan sauyin yanayi, ciki har da matakan tabbatar da adalci a yaki da sauyin yanayi, da kuma sabon tsarin samar da kudaden cimma nasarar hakan.

Cikin jawabin da ya gabatar, shugaban kasar Kenya William Ruto, ya ce sanarwar za ta share fagen shawarwarin da nahiyar Afirka za ta shiga, yayin taron sauyin yanayi na MDD wanda za a gudanar a ranar 20 ga watan nan na Satumba a birnin New York, da taron COP28 na watan Nuwamba, wanda zai gudana a hadaddiyar daular Larabawa.

Shugaba Ruto ya kara da cewa, Sanarwar Nairobi, matsaya ce ta bai daya ga dukkanin kasashen nahiyar, kuma kuduri ne dake tabbatar da jajircewar nahiyar, da aniyar bude sabon babi na shiga ayyukan yaki da sauyin yanayi na duniya, da ajandar ci gaba mai dorewa, wanda hakan zai baiwa sauyin da ake fatan samu a makomar tattalin arziki da zamantakewar duniya wani yanayin musamman na Afirka.

Kaza lika, mista Ruto ya bayyana sanarwar a matsayin wadda ta fayyace, da yayata matsayin Afirka, game da hanyoyin da suka kamata a bi wajen shawo kan kalubalen sauyin yanayin, da ma muhimman ka’idojin da ya kamata sassan kasa da kasa su bi, wajen tabbatar da nasarar wanzuwar manyan bukatun tattalin arziki, da na kare muhallin halittun dake kewaye da bil adama.  (Saminu Alhassan)