logo

HAUSA

Shugaban majalisar mulkin Sudan ya ba da dokar rusa dakarun RSF

2023-09-07 09:20:41 CMG Hausa

 

            

Shugaban majalisar mulki ta rikon kwarya ta kasar Sudan, kuma babban kwamandan sojojin kasar, Abdel Fattah Al-Burhan, ya gabatar da doka kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada, na rusa rundunar sojojin kai daukin gaggawa ta kasar (RSF).

A cewar wata sanarwa da majalisar mulkin kasar ta fitar, Al-Burhan ya umurci babbar hedkwatar rundunar sojojin Sudan, da babbar sakatariyar majalisar mulkin kasar, da sauran hukumomin da abin ya shafa, da su aiwatar da hukuncin.

Sanarwar ta bayyana cewa, an yanke shawarar ce bisa sakamakon bijirewar da sojojin na RSF suka yi wa kasar, da manyan laiffukan cin zarafi da suka aikata kan ‘yan kasar Sudan, da yi wa kayayyakin more rayuwa na kasa zagon kasa da gangan, baya ga karya manufofin kafa su, da ayyukan da aka dora musu, da ka’idojin da ke kunshe a cikin dokar da ta kai ga kafa rundunar kai daukin gaggawa ta shekarar 2017.(Ibrahim)