logo

HAUSA

An yi bikin murnar cika shekaru 10 da gabatar da shawarar zirin tattalin arziki na hanyar siliki

2023-09-07 10:25:14 CMG Hausa

Domin tunawa da cika shekaru 10 da gabatar da shawarar zirin tattalin arziki na hanyar siliki, kafar CGTN ta babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin, ta yi hadin gwiwa tare da ofishin jakadancin Sin dake kasar Tanzania, wajen gudanar da bikin musamman mai taken “Sabon tafarki kan raya hanyar siliki, wato hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka”. Wakilai daga bangarori daban daban na kasashen Afirka fiye da 200 sun halarci bikin, inda suka waiwayi hadin gwiwar Sin da Afirka wajen neman raya makoma ta bai daya tsakanin Sin da Afirka, da nuna kyakkyawar makoma ta raya shawarar ziri daya da hanya daya bisa sabon tafarki.

Mataimakin shugabar majalisar dokokin jama’ar kasar Tanzania Hon. Mussa Zungu ya bayyana cewa, muhimmin aiki na raya kasashen gabashin Afirka, shi ne kara yin mu’amala, da gina ayyukan sufuri, kuma an kawo babbar dama ga gabashin Afirka, karkashin shawarar ziri daya da hanya daya a cikin shekaru 10 da suka gabata. Kana hakan ya sa kaimi ga kasashen gabashin Afirka, wajen rike damar shawarar ziri daya da hanya daya, domin cimma burin bunkasuwar tattalin arzikinsu. (Zainab)