logo

HAUSA

Kamfanonin Afirka 10 za su yi takarar lashe lambar yabo ta “Gwarzon Kasuwanci” na shekarar 2023

2023-09-06 10:35:20 CGTN HAUSA

 

An gudanar da zagayen kusa da na karshe, na tantance kamfanoni daga kasashen Afirka, wadanda za su fafata a gasar lashe lambar yabo ta “Gwarzon Kasuwanci” na shekarar 2023. Bayan tantance sama da kamfanoni 27,000 daga kasashen Afirka 54, yanzu haka an ware kamfanoni 10, da za su fafata a zagayen karshe na lashe kambin “Gwarzon Kasuwanci” na shekarar 2023, wato Africa's Business Heroes ko ABH a takaice.

Mashirya gasar sun ce za a gudanar da zagayen karshe na gasar ne tsakanin ranaikun 23 da 24 ga watan Nuwamba mai zuwa, a birnin Kigalin kasar Rwanda, inda ake sa ran kamfanin da ya yi nasara zai samu kyautar kudi har dalar Amurka miliyan 1.5.

Wata sanarwar da ABH din ta fita a ranar Litinin, ta ce gidauniyar Jack Ma ce ke daukar nauyin gasar, kuma a ranar Juma’a da Asabar din karshen makon jiya ne aka gudanar da zangon kusa da na karshe na gasar a birnin Kigali.

Kamfanoni 10 da za su fafata a zagayen karshe na wannan gasa, sun fito ne daga kasashen Afirka 8, wato Benin, da Masar, da Ghana, da Kenya, da Morocco, da Najeriya, da Rwanda da Afirka ta kudu.  (Saminu Alhassan)