logo

HAUSA

Tawagar Sudan za ta halarci babban taron MDD karo na 78

2023-09-06 09:44:47 CGTN Hausa

 

Tawagar kasar Sudan karkashin jagorancin shugaban kwamitin rikon kwarya na kasar kuma babban kwamandan sojojin kasar ta Sudan, Abdel Fattah Al-Burhan, za ta halarci zaman babban taron MDD karo na 78 da zai gudana a birnin New York na kasar Amurka.

Ma'aikatar harkokin wajen Sudan ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar jiya Talata cewa, ministan kudi da tsare-tsaren tattalin arziki na kasar, Jibril Ibrahim zai raka Al-Burhan wajen babban taron majalisar.

Tawagar ta kuma hada da mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Ali Al-Sadiq, da darektan hukumar leken asirin kasar, Ahmed Ibrahim Mufadel.(Ibrahim)