logo

HAUSA

An rantsar da shugaban kasar Zimbabwe

2023-09-05 09:56:15 CMG Hausa

Shugaban kasar Zimbabwe mai ci Emmerson Mnangagwa ya sha rantsuwar kama aiki a jiya Litinin, gaban jagororin yankunan kasar, da ma manyan baki daga kasashen waje. Yanzu haka shugaba Mnangagwa zai zarce kan karagar mulki na tsawon karin shekaru 5, bayan da ya lashe babban zaben da ya gudana a watan da ya gabata, da kashi 52.6 bisa dari da jimillar kuri’un da aka kada.

Cikin jawabinsa na shan rantsuwa, mista Mnangagwa ya godewa al’ummar Zimbabwe, bisa yadda suka ba shi damar ci gaba da jagorancin kasar. Yana mai shan alwashin ci gaba da dinke kasar, da zamanintar da ita, da kawo ci gaba cikin shekaru 5 masu zuwa.

Shugaban Zimbabwe ya kuma ce karkashin sabon wa’adin jagorancinsa, zai gaggauta bunkasa yankunan karkara, kana zai karfafa fannin samar da isasshen abinci, da zamanintar da ababen more rayuwa, da ingiza fannonin sarrafa hajojin kasar da samar da makamashi.

Ya ce Zimbabwe a shirye take ta karfafa kyakkyawar alakarta da sauran kasashen duniya.  (Saminu Alhassan)